Mai magana da yawwun hedkwtar sojojin Najeriya Birgediya Janar Rabe Abubakar dalilin yin hakan shi ne yaki da ta'addanci ba yaki ba ne na kasa daya.
Manyan kasashe ma suna bukatar taimakon kananan kasashen domin a ci karfin 'yan ta'ada koina suke.. Yaki da ta'adanci ya koma na kasa da kasa. Saboda haka kowace kasa ta kawo shawara Najeriya tana maraba da ita.
Kwararrun sojoji ne zasu je Najeriya wadanda zasu hada karfi da karfe su tabbatar an samu nasara.
A wani sabon yunkurin yaki da ta'adanci rundunar sojojin Najeriya ta kaddamar da rukunin sojojinta a zaman mayaka akan babura a yankin na arewa maso gabas omin bin sawun 'yan ta'adan.
Inji Kanar Kukasheka an ci karfin 'yan Boko Haram saboda haka galibinsu sun koma suna fashi da makami ne tare da shiga lunguna lunguna suna barna. Dalili ke nan da sojoji suka fito da salon yin anfani da babura domin iya shiga duk sakon da aka ji labarinsu. Dalili na biyu shi ne bude hanyoyin da aka daina anfani dasu domin 'yan Boko Haram. Masu babura su ne zasu dinga kula da hanyoyin suna sintiri.
Ga karin bayani.