Dan Majalisar Dattijai Senata Bukar Abba Ibrahim, wanda wakili ne a majalisar dokokin kasashe da suke yammacin Afirka, yace kwamitin majalisar ta zartas kuduri da zai wajabtawa duk kasashe dake yankin, suyi aiki da kudurorin da majalisar da zartas, mai makon halin da ake ciki yanzu na zabi, ko kasa ta yi , ko ta bari.
Wannan yana daga cikin kudurori biyu da kwamitin ya zartas a zaman da ya gudanar a Abuja.
Senata Abba Ibrahim, yace, kuduri na biyu kuma shine, maimakon halin da aka ciki na shugabannin majalisun suke zaben wakilai da zasu wakilci kasashensu a majaisar wakilan, yanzu sai an gudanar da zabe.
Sai dai baiyi bayani ko a majalisun ne za'a gudanar da zaben, ko kuma jama'a ne zasu sake zabensu.
Da yake sharhi kan haka, wani mai nazari kan al'amuran yau da kullum, Buhari Bello Jega, yace, wannan mataki yana da kyau, domin ana zamanin demokuradiyya ne, bai kamata shugabannin majalisu su kasance wadanda zasu zabi wakilan ba, gudun kada son zuciya ya shigo cikin al'amarin.
Ga rahoto.
Your browser doesn’t support HTML5