Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masar: An Yankewa Morsi Hukuncin Kisa


Tsohon shugaban Masar, Muhammed Morsi a tsare a gidna kurkuku
Tsohon shugaban Masar, Muhammed Morsi a tsare a gidna kurkuku

Wata kotun kasar Masar ta yankewa tsohon shugaban kasar Muhammed Morsi da wasu mutane 100 hukuncin kisa, bayan da aka same su da laifin fasa wani gidan yari da aka yi a shekarar 2011.

A dai yau Asabar ne kotun ta yanke wannan hukuncin a birnin Alkahira bayan da aka kwashe wani tsawon lokaci ana shari'a.

A ranar biyu ga watan Yuni, ake sa ran babbar hukumar addinin kasar da ake cewa Mufti, za ta fadi matsayarta game da wannan hukunci, wanda hakan zai bayyana matsaya hukunci a karshe.

Har ila yau an tuhumi Morsi da laifin yin leken asiri a shari’ar da aka mai.

A watan da ya gabata, aka yankewa Mr Morsi, wanda ya kasance zababben shugaban kasar na farko, hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 20, bayan da aka dora mai alhakin mutuwar wasu masu zanga zanga a wajen fadar shugaban kasar a shekarar 2012.

Kotun har ila yau ta sami wasu shugabannin kungiyar ‘yan uwa musulmi ta Muslim Brotherhood da wasu masu mara mata baya su 12 da laifin ta da tarzoma, ba na kisa ba.

Sojojin kasar ta Masar, sun hambarar da gwamnatin Mr Morsi ne a shekarar 2013, bayan da miliyoyin mutane suka yi zanga zanga, suna zargin gwamnatin ta Morsi da cewa ta wuce gona da iri a harkokin mulki.

Tun daga lokacin, gwamnatin tsohon shugaban dakarun kasar, Abdel Fata el-sisi, wanda shi ne shugaban kasar na yanzu, ta kulle dubban ‘yan kungiyar Muslim Brotherhood da magoya bayanta.

XS
SM
MD
LG