Kakakin rundunar ‘yan sanda Emmanuel Ojukwu ya kara da cewa shingayen kan haifar da damuwa ga yanayin muhallanmu.
“Sannan baya ga haka wurare ne da wasu daga cikin jami’an mu marasa kishin kasa ke karbar na goro da takurawa jama’a, a wani sa’in ma har a bindige mutane. Saboda haka shugaban ‘yan sandan Najeriyar ya ga ya dace ya ba da umurnin janye wadannan shingaye.” In ji Ojukwu.
Tuni dai masu ruwa da tsaki a harakar sufuri suka fara tofa albarkacin bakinsu kan wannan lamari, inda wasu ke cewa shingayen suna da amfani da kuma rashin amfani.
“Magana ta gaskiya wadannan shingaye suna da amfaninsu kuma suna da rashin amfani, amfaninsu shi ne sukan taimaka wajen gane bata gari akan manyan hanyoyin kasar nan amma kuma rashin amfanisu shi ne ana karbar cin hanci da rashawa, domin mafi yawan ‘yan sanda na karba.” In ji Alhaji Sani Gamko, mai sharhi kan ababan sufuri.
To sai dai duk da wannan umurni, wasu matuka na cewa har yanzu ba a janye shinagyen binciken ba kamar yadda wani direba mai suna Malam Ali ya gayawa Muryar Amurka.
“Gaskiya tsakani da Allah ba a janye ba kuma gaskiya suna takura mana, suma kansu ‘yan sandan su kan ce mu ajiye motar mu mu nuna musu takardaunmu, in muka nuna musu sai su ce mu kawo wani abu.” In ji Malam Ali.
Rundunar ‘yan sandan dai ta ce babu wata doka da ta hana su kafa shingayen bincike, amma kuma kasancewar ‘yan sanda akan hanya na zama barazana ga masu shirin aikata miyagun laifuka.
“Amma yanzu an yi la’akkari da irin illolin da shingayen binciken ke haifarwa.” Ojukwu ya kara da cewa.
Sannan Kakakin ‘yan sandan ya musanta cewa har yanzu akwai shingayen akan hanya yana mai cewa dole ne abi umurnin Inspeto Janar din na ‘yan sanda.
Ga karin bayani a rahoton da Hassan Maina Kaina ya hada mana: