Sakamkon kisan da ake zargi kan 'gubar dalma' a jihar Nija dake arewa maso tsakiyar Nijeriya, Gwamnan jihar mai jiran gado, Alhaji Abubakar Sani Bello yace gwamnatinsa zata dauki mataki na hana wannan al'amari sake aukuwa.
A makon jiya ne dai aka bada rahoton gubar dalmar ta kashe kusan mutane 30 a jihar, abunda masana kiwon lafiya suka danganta da aikin hakar ma'adinai shigen abunda ya faru a jihar Zamfara cikin 'yan shekarun nan.
Gwamnan mai jiran gado yace, matakin da gwamnatinsa zata dauka ba zai takurawa mutanen da suka dogara ta wannan hanya wajen neman abinci ba.
Daga nan Alhaji Abubakar Sani Bello ya mika ta'ziyyarsa ga iyalan wadanda wannan fitina ta rutsa da su.
A nasa bangaren daya daga cikin masu kamfanoni da suke hakar ma'adinan Alhaji Danladi Sarkin Daji, ya aza laifin gubar daga 'yan kasar Nijar wadanda suka kawo gubar suna amfani da shi wajen wanke zinari.
Yace ba'a yi musu adalci ba idan aka hana su aikinsu ganin sun nunawa hukumomi sarsalar gubar.
Da yake magana kan binciken da suke yi gameda wannan batu Darekta a matakin farko Dr. Mahmud Usman, yace tuni sun gayyato kwararru ciki har da likitoci daga kungiyar nan ta kasa da kasa da ake kira "Doctors Without Borders" da kuma wasu daga cibiyar da ake kira NCDC domin su taya su kara gano wannan cuta.
Ga rahoto