Kungiyar kabilu da suke arewa maso yamma, yanki da aka fi sani da 'Middle -Belt', sunyi kira ga Majalisar Dinkin Duniya tasa baki su sami 'yancin kai daga Najeriya, saboda abunda shugabanninta suka kira ci gaba da kisan gilla da ake yiwa jama'arta.
Shugaban kungiyar Toma Davou, wanda yayi wannan kira yace kungiyar zata je Majalisar ta Dinkin Duniya domin neman 'yancin kai, domin ba zasu iya ci gaba da zama da mutane da suke yi musu kisan gilla ba.
Mr. Davou yace an kashe akalla mutane milyan biyu daga shekara ta 1994 lokacinda wannan rikici ya barke.
Da aka tambayeshi irin matakai da suka dauka na neman kawo karshen wannan tashe tashen hankula, Mr. Davou, yace babu irin bincike da ba'a gudanar ba tun lokacinda aka fara wannan rikici, amma har zuwa yanzu babu sauki.
Yace, kamar yadda aka baiwa Sudan ta kudu 'yancin kai, su ma a basu 'yanci, domin suna da arzikinsu, da mutane masu ilmi, ba tilas ne sai suna da mai ko arzikin dabbobi ba.
Da aka tuntubeshi kan rikici da ya kai ga wadannan tashe tashen hankula, daya daga cikin masu ruwa da tsaki a yankin, Ustaz Ibrahim Barikin Ladi, yace suna gudanar da tarurruka tsakanin shugabannin addinin kirista da na Islama domin wayar da kan jama'a cewa wajibi ne a sami zaman lafiya kamin a sami ci gaba.
Usaz Ibrahim ya kara da cewa akwai bukatar a tuntubi sarakunan gargajiya, kungiyoyin matasa da mata domin su gane cewa babu addini da yarda da kashe kashe da lalata dunika.
Shugabar karamar hukumar Riyom Madam Josephine Piyo, tace maharan sun bullo da sabon salo na kai hare hare ta wajen kwashe abinci da dabbobi, da katifu, kamin su cunnawa gidaje wuta.
Tace a matsayinta na uwa ga dukkan al'umar dake yankin, zata ci gaba da tuntuba ga duka sassan, da nufin maido da zaman lafiya kamar yadda yake ada.
Ga Zainab da rahoto