Bayan ta koma bakin aiki jiya talata, majalisar dattijan Najeriya ta tafka muhawara kan batutuwa daban daban, musaman ma dai kan batu dage zabe da hukumar zabe tayi.
Da yake magana da wakiliyar Sashen Hausa Madina Dauda, Senata Hadi sirika, dan jam'iyyar hamayya ta APC yace babu harkar soja da batun zabe, doka bata yi wannan tanadi ba, amma idan har za'a yi haka sai an gabatarwa majalisar dokoki wannan bukata daga bangaren shugaban kasa, idan har Majalisa tayi na'ama da matakin kamin a tsoma su cikin harkokin zabe.
Domin haka ne majalisar take neman shugaban hukumar zabe Parfessa Attahiru Jega ya bayyana a gaban majalisar laraban nan domin yayi mata karin bayani kan dage zaben.
Daga bisani wakilai daga jam'iyyar hamayya suka yi taro da manema labarai ind a suka na'am da bullo da na'urar da zata tantance katin zabe cewa wanda yazo da ita, hakika shine mai ita.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5