A cewar sakataren kasa na jam'iyyar APC Mai Mala Boni akwai ayar tambaya kan hujjojin da aka bayar.
Yayinda shugaban kasa ke tattaunawa da sakataren harkokin wajen Amurka Johan Kerry ya bashi tabbacin za'a gudanar da zabe ranar 14 ga wannan watan. Shin shugaban bai yi shawara da hafsan hasoshin sojoji ba ne lokacin. Idan a lokacin ya san jami'an tsaro ba zasu iya bada tsaro ba me yasa ya bada tabbacin za'a gudanar da zubbukan a lokacin da aka shiryasu.
Hafsoshin sojojin kasar sun zauna sun tabbatarwa kasa cewa a shirye suke za'a gudanar da zaben. Sai kwatsam cikin dan kankanin lokaci sai aka sake rawa wai domin sojoji ba zasu iya bada tabbacin tsaro ba..
To saidai dan kwamitin kemfen din shugaba Jonathan Abdullahi Bala Kano ya musanta zargin 'yan adawan. Yace duk wani shiri da INEC tayi tun shakarar 2014 babu abun da ta nema da gwamnati bata bata ba. Zancen cewa PDP nada hannu a dage zaben ba gaskiya ba ne. Maganganu ne da mutane keyi bisa ga jahilci.Yace zance ne na tsaro ba wai PDP tana tsoron a gudanar da zabe ba.
Ga rahoton Medina Dauda.