Hukumar zaben INEC mai zaman kanta, tayi kira ga 'yan Najeriya su tashi tsaye wajen ganin sun karbi katunan zabensu na din din din. A yayinda yanzu take kokarin ganin ta kammala rarraba su.
Kakakin hukumar zabe ta kasa reshen jihar Flato, Osaretin Omahiyeriyebo, yace akwai dokoki da aka tanadar kan masu saye ko sayar da katunan zabe. Yace masu aikata wannan laifi suna fuskantar dauri ko tara ko duka biyu na tsawon shekaru biyu, da tarar Nairea dubu dari biyar.
Gameda raba katunan zaben, Osaretin yace, hukumar a jihar Flato tana fuskantar matsaloli wajen raba katunan zaben a kananan hukumomin Kanke, da Jos ta kudu, da kuma Langtang ta arewa da langtang ta kudu. Wadannan kananan hukumomi har yanzu ba'a buga katunansu ba. Amma Osaretin ya bada tabbacin cewa nan da takwas ga wata kowa zai karbi katinsa.
Wakiliyar Sashen Hausa Zainab Babaji ta zanta da wani da har yanzu bai sami katinsa ba. Da kuma wani ndan siyasa kan batun saye ko sayar da katunan zabe.