Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Masoya APC Sun Yi Zanga-zanga a Adamawa


Magoya bayan APC
Magoya bayan APC

Magoya bayan APC dauke da kwalaye sun gudanar da zanga-zangar lumana akan yadda hukumomin gwamnatin tarayya ke kama 'yan siyasarsu suna kulle wa

Dubun dubatansu ne suka fantsama kan manyan titunan fadar gwamnatin Adamawa tare da nuna bacin ransu.

Suna zargin hukumar EFCC da kamun dauki daidai da suka ce hukumar na yiwa wasu kusoshinsu. Duk da kamun sun ce su ba zasu razana ba. Mutanen suna zargin ana yi masu cin fuska da kame-kame.

Ranar Juma'ar da ta gabata jami'an hukumar EFCC suka yi awon gaba da Kwamondo Abdulaziz Nyako dan tsohon gwamna Murtala Nyako da aka tsige kuma dan takarar kujerar sanata a karkashin APC. Hukumar tana cigaba da neman mahaifinsa ruwa a jallo ta kamashi.

Magoya bayan jam'iyyar sun ce ba gudu babu ja da baya koda ma za'a kama duk 'yan takarar jam'iyyar ne.

To saidai kuma yau a ke zaton kutun daukaka kara zata yanke hukunci akan karar da kakakin majalisar ya shigar inda yake neman a sake mayar dashi a kan kujerar mukaddashin gwamnan jihar. Yana rokon kotun ta cire Barrister Bala Ngilari daga kujerar gwamnan jihar.

Tsigeshin ka iya bude wani sabon babi a siyasar jihar.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG