Tsohon shugaban kasar Nijeriya Cif Olusegun Obasanjo ya bar jam’iyyarsa ta PDP tare da yaga katinsa na rijistar zama dan jam’iyyar. Yace jam’iyya mai mulkin kasar ta dage zabe ne don magudin shigo da gwamnatin rikon kwarya, inda yace Allah ba zai basu sa’a ba. A kwanakin baya Obasanjo ya zargi Shugaban Nijeriya Jonathan da son kawo kunbiya-kunbiyar da zata sa ya dade akan mulki irin su shugaba Laurent Gbagbo na Kasar Cote D’Ivoire.
Kakakin jam’iyyar PDP Olisa Metuh ya bayyana ficewar Obasanjo daga jam’iyyar a matsayin koma baya. Haka zalika sanarwar da ya fitar a madadin jam’iyyar PDP bata bi ta kan maganar korar da reshen jam’iyyar PDP na Jihar Ogun ya yiwa Obasanjon ba sa’o’i da dama bayan fitacewarsa. Abdulkarim Dayyabu shine shugaban Kungiyar Adalci ta Nijeriya, ya bayyana cewa in dai har kamar Olusegun zai fita daga jam’iyya PDP da ta yi masa komai a rayuwa to kuwa bai ga dalilin da wani mai hankali zai zauna a cikin jam’iyyar ba.
Wasu ‘yan jam’iyyar PDP na ganin cewa ficewar tsohon shugaban kasar daga cikinta ba zai shafi zaben kasa mai zuwa ba, suna ma ganin cewa hakan zai basu damar kauda kai daga kan Obasanjon da ya zame musu alakakai. Injiniya Sa’ad Abdullahi na daga jiga-jigan yakin neman zaben Muhammadu Buhari a jam’iyyar APC.
Shima yace fitar Obasanjo daga PDP abin jin dadi ne don zai kawo musu gibi mai wuyar cikewa. Shi kuwa kakakin yakin neman zaben Goodluck, Femi Kayode cewa yayi, Obasanjo ya barsu ne saboda Goodluck ya ki yarda ya zamar masa rakumi da akala.