Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai ziyarar jaje karamar hukumar Chibok.
Zulum ya kai ziyara ne bayan wasu hare-hare da mayakan Boko Haram/ISWAP suka kai garuruwan Kawtakare, Korohuma da Pemi a karamar hukumar ta Chibok.
Wata sanarwa da gwamnatin ta fitar a shafinta na Facebook a ranar Talata ta ce gwamna Zulum ya gana da iyalan mutanen da aka sace.
“Gwamnan ya hadu da iyalan wadanda Boko Haram/ISWAP suka sace - mata 22 da maza biyu a wani masaukin gwamnati da ke garin na Chibok.
“Mun zo ne don mu jajinta muku da iyalan ‘yan uwanmu mata da maza da aka sace, da wasu mutum hudu da ‘yan ta’addan Boko suka kashe a wannan abin alhini. Mu ma mun ji zafin wannan al’amari muna kuma addu’ar hakan ba zai sake faruwa ba.” Sanarwar ta ce.
Mayakan sun kai harin ne a ranar 21 ga watan Janairun 2022 a Kawtakare sai kuma wanda suka kai Pemi a ranar 14 ga watan Janairu da wani hari da aka kai Korohuma a ranar 30 ga watan Disambar bara.
Yayin ziyarar Zulum ya kuma gana da manyan jami’an tsaron da ke yankin.
A shekarar 2014 mayakan na Boko Haram sun sace ‘yan mata dalibai sama da 270 a makarantar sakandaren Chibok, lamarin da ya janyo kakkausar suka daga sassan duniya.
A lokacin harin, wasu daga cikin daliban sun tsere, an kuma yi nasarar karbo wasu yayin da har yanzu akwai ragowar wadanda ba a gan su ba.