Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ISWAP Ta Tabbatar Da Mutuwar Abubakar Shekau


Abubakar Shekau, Shugaban Kungiyar Boko Haram
Abubakar Shekau, Shugaban Kungiyar Boko Haram

“Shekau ya zabi azaba da wulakancin lahira akan na duniya, shi ya sa ya kashe kansa nan take, ta hanyar tarwatsa kansa da bam.”

Makonni biyu bayan bullar rahotannin da ke bayyana cewa shugaban kungiyar Boko Haram ya mutu, kungiyar mayakan IS ta yankin Afirka ta yamma wato ISWAP, ta yi ikirarin cewa Abubakar Shekau ya mutu.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa ya sami wani sautin murya daga hannun da ya ke samun sakonnin da suka gabata na kungiyar, inda shugaban ISWAP din Abu Musab Al-Barnawi, yake tabbatar da cewa Shekau ya kashe kansa ne ta hanyar tayar da bam da ke jikinsa.

Abubakar Shekau, Shugaban Kungiyar Boko Haram
Abubakar Shekau, Shugaban Kungiyar Boko Haram

A cikin sakon muryar, Al-Barnawi ya ce ISWAP ta aike da mayakanta a dajin Sambisa inda suka kai farmaki ga shugaban na Boko Haram, inda “daga nan ya sami arcewa ya buya a cikin jeji tsawon kwana 5.”

Al-Barnawi ya ci gaba da cewa “mayakanmu sun ci gaba da farautarsa, suka kuma gano shi, kana suka nemi da ya tuba ya mika wuya, amma kuma sai ya ki, a maimakon haka ya kashe kansa.”

Karin bayani akan: ​Al-Barnawi, ISWAP, ​Boko Haram, Abubakar Shekau, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

“Shekau ya zabi azaba da wulakancin lahira akan na duniya, shi ya sa ya kashe kansa nan take, ta hanyar tarwatsa kansa da bam.”

“Mun yi farin ciki da haka” in ji muryar ta Al-Barnawi, “Shekau mutum ne da ya aikata munanan ayyukan ta’addanci.”

Har kawo yanzu dai kungiyar Boko Haram ba ta ce komai ba a hukumance dangane da mutuwar shugaban na ta, wanda ya kwashe shekara fiye da 10 yana haddasa ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso gabashin Najeriya da makotan kasar.

Sai dai har yanzu, rundunar sojin Najeriya, ta ce tana ci gaba da bincike akan ikirarin mutuwar ta Shekau.

Rundunar Sojojin Nijeria Sun Sha Alwashin Cigaba Da Farautar Yan Boko Haram
Rundunar Sojojin Nijeria Sun Sha Alwashin Cigaba Da Farautar Yan Boko Haram

Wannan kuma ba shi ne karo na farko da ake ba da rahoton mutuwar shugaban na Boko Haram ba tsawon shekaru 12, amma daga bisani kuma ya bayyana a sakon bidiyo yana karyatawa.

Ayyukan kungiyar ta Boko Haram sun kara kamari ne bayan sace dalibai 270 a garin Chibok a shekarar 2014, lamarin da ya ja hankalin duniya baki daya, har aka shiga gangamin neman kubutar da daliban.

Da farko kuma ISWAP sashe ne na kungiyar ta Boko Haram, amma kuma daga bisani a shekarar 2016 ya balle tare da yin mubayi’a ga kungiyar IS.

Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji
Boko Haram ta yi ikirarin kakkabo jirgin saman soji

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito masu fashin baki na bayyana ra’ayin cewa mutuwar ta Abubakar Shekau kan iya kawo karshen takaddama tsakanin kungiyoyin biyu na ISWAP da Boko Haram, wanda kuma zai baiwa ISWAP din damar mamaye Boko Haram, domin ta kara kwari da mamayarta a arewa maso gabas.

XS
SM
MD
LG