Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Muka Kwashe Kwanaki Muna Tafiya A Daji - Matan Da Suka Kubuta a Hannun Boko Haram


Matan da suka kubuta daga hannun Boko Haram a lokacin da ake gabatar da su ga gwamna Zulum (Facebook/Gwamnatin Borno)
Matan da suka kubuta daga hannun Boko Haram a lokacin da ake gabatar da su ga gwamna Zulum (Facebook/Gwamnatin Borno)

“Mata shida da yaransu tara suka tsere daga hannun mayakan,” a cewar Kwamishinar mata Zuwaira Gambo.

Gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ce wasu mata da yara da mayakan Boko Haran suka yi garkuwa da su a tsakanin shekarar 2020 zuwa bana a wasu Coci-coci, sun kwashe kwana shida a daji suna tafiyaa kafa bayan da suka tsere daga hannun ‘yan ta’addan.

Wata sanarwa da gwammatin jihar ta fitar ta ce an mika mata da yara 15 wadanda suka samu kubuta daga hannun mayakan na Boko Haram.

“Mata shida da yaransu tara suka tsere daga hannun mayakan,” a cewar Kwamishinar mata Zuwaira Gambo.

Uku daga cikin matan da suka hada da Rachel Simon, Esther Ayuba an yi garkuwa da su ne a Tukalashi da ke karamar hukumar Chibok yayin da Alheri Ezikiel, Victoris Andrew da Victoria James an sace su ne a kauyen Cofure da ke karamar hukumar Hong a jihar Adamawa.

Hukumomin jihar ta Borno sun bayyana cewa, matan sun yi amfani da mika wuya da wasu daga cikin ‘yan Boko Haram ke yi suka sulale suka gudu.

Cikin sanarwar, gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum da ya karbi mutanen a fadar gwamnati, ya nuna farin cikinsa da samun kubuta da matan suka yi.

Ya kara da cewa, gwamnati za ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin an kubutar da duk sauran mutanen da ke hannun mayakan kungiyar ta Boko Haram.

Gwamnan har ila yau ya gabatara da matan da yara ga shugaban kungiyar Kiristoci ta CAN reshen jihar Borno Rev. Mohammed Naga da tawagarsa.

XS
SM
MD
LG