Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Mu Manta Da 'Yan Matan Chibok Ba - Buhari


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Fadar Shugaban Najeriya ta ba da tabbacin cewa, ba ta manta da 'yan mata daliban Chibok da aka sace a shekarar 2014 ba, tana mai cewa a ko da yaushe, tana tunaninsu kamar yadda iyayensu suke yi.

Cikin Wata sanarwa da fader ta fitar dauke da sa hannu kakakin Shugaba Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, fadar ta ba da tabbaicn cewa har yanzu ana nan ana kokarin ganin an kubutar da daliban.

“Babu wanda ya cire rai. Har yanzu jami’an tsaro da masu tattara bayanan sirri na bin hanyoyin da ya kamata domin ganin an sake su.” Sanarwar ta ce.

“Nasarorin da sojojinmu ke samu a ‘yan kwanakin nan akan ‘yan ta’adda, na ba mu kwarin gwiwar cewa akwai alamun za a iya samun nasara a kowane lokaci.”

Saboda haka, fadar ta ce, tana bukatar a ba sojojin kasar goyon baya a kuma taya su da addu’a yayin da suke gudanar da ayyukansu na kokarin ganin sun gama da ‘yan ta’addan tare da kubutar da duk wadanda ake tsare da su.

Lokacin da Buhari yake ganawa da wasu daga cikin 'yan matan Chibok da aka kubutar a 2017
Lokacin da Buhari yake ganawa da wasu daga cikin 'yan matan Chibok da aka kubutar a 2017

Wannan sanarwar da fadar gwamnatin ta Najeriya ta fitar, na zuwa ne yayin da ragowar ‘yan matan na Chibok suka cika shekara bakwai cif da bata.

Wata sanarwa da kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta fitar a Twitter a ranar Laraba, ta nuna takaicinta kan yadda hukumomin kasar suka gaza kubutar da ‘yan matan.

Karin bayani akan: Chibok, Boko Haram, Amnesty International, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

“Yau shekara bakwai kenan da Boko Haram ta sace dalibai mata 279 a garin Chibok,” Amnesty ta ce a shafinta na @AmnestyNigeria.

Sojojin Najeriya a dajin Sambisa
Sojojin Najeriya a dajin Sambisa

Kungiyar ta ce, ko da yake, wasunsu sun tsere yayin da aka sako wasu, “amma har yanzu ana garkuwa da ragowar dalibai sama da 100.”

Amnesty ta kara da cewa fargabar sace dalibai, ta sa an rufe makarantu da dama a yankin arewacin kasar.

“Duk irin matakin da gwamnatin ke dauka wajen ganin an shawo kan wannan lamari, ba ya aiki.”

“Dubun dubatar dalibai ba sa samun damar zuwa makaranta, saboda gazarawar da hukumomi suka yi wajen samar da tsaro a makarantu musamman a arewacin Najeriya.”

XS
SM
MD
LG