Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Sake Jefa Maiduguri Cikin Duhu


Wata tashar wutar lantarki a Najeriya.
Wata tashar wutar lantarki a Najeriya.

Mayakan Boko Haram sun sake lalata wasu turakun wutar lantarki a Maiduguri babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Hakan ya jefa da yawa daga cikin jama’ar birnin cikin duhu saboda turakun wutar lantarkin da mayakan suka lalata. Wannan dai ba shi ne karon farko da mayakan suke lalata wadannan kayan wutar ba.

A watan Janairu sun kai harin kan turakun wutar lantarki, lamarin da ya sa sai da aka kwashe kusan wata biyu ana aikin gyaran wutar

Rahotanni sun ce kwana uku kenan da aka gyara wutar, wanda aikin ya gudana karkashin tsauraran matakan tsaro.

Yankin da a mayakan na Boko Haram suka lalata turakun wutar na da nisan kilomita 50 daga birnin na Maiduguri.

Sojojin Najeriya a lokacin da suka baje wasu makamai da suka kama (Hoto: Nigerian Army Twitter)
Sojojin Najeriya a lokacin da suka baje wasu makamai da suka kama (Hoto: Nigerian Army Twitter)

Wannan lamari na faruwa ne, yayin da dakarun Najeriya karkashin rundunar “Operation Lafiya Dole” ta ce ta kashe da yawa daga cikin mayakan kungiyar a yankin garin Chibok.

Rundundar sojin ta samu wannan nasara ce bayan wani kofar-rago da ta yi wa mayakan, wadanda bayanan sirri suka ce suna ta tserewa, saboda galaba da ake samu akan su.

Karin bayani akan: Boko Haram, Chibok, Maiduguri, Nigeria, da Najeriya.

“Jaruman dakarunmu, sun yi musu kwantan-bauna, suka far musu da karfin gaske, suka kashe mayaka 9 yayin da wasu dama suka tsere da harbin bindiga a jikinsu.” Wata sanarwa da sojojin suka fitar dauke da sa hannun jami’in yada labarai Brigadier General Mohammed Yerima ta ce.

“Hakazali mun yi nasarar kwato bindigar AK 47 guda takwas da harsashai da dama, kuma yanzu dakarunmu sun karbe ikon yankin.” Sanarwar ta kara da cewa.

Wannan kwantan-bauna da dakarun Najeriyan suka ce sun yi wa mayakan, ya faru ne a tsakanin Chibok zuwa Damboa.

XS
SM
MD
LG