Kamar yadda shirin samartaka na wanna makon ya kawo maku ra’ayoyin matasa maza da mata akan batutuwa da dama da suka shafi rayuwa da zamantakewar matasa a wurare daban daban.
A wannan makon mun sami tattauna ne akan yadda wasu ‘yan mata suka rungumi dabi’ar sa dogon wando matsattse wanda aka fi sani da Legins a turance, har ma su fita cikin al’uma ba tare da jin kunya ko nauyin irin kallon da jama’a zasu yi masu ba.
Ta dalilin haka ne muka sami zantawa da kwararren malami a sashin zamantakewa da nazarin halayyar dan’adam Dr Abudullahi Mai Kano Madaki na jami’ar Bayero dake birnin Kano inda yayi mana cikakken bayani akan yadda wannan dabi’a ta samo asali, da illolinta tare da bada shawarwari.
A cikin bayanansa, ya bayyana cewar wannan al’ada ta sa wando ta yi karo da al’adu da addinan yawancin jama’ar arewacin Najeriya, domin kuwa bata daga cikin al’adun da aka sani, wannan na nanufin aron al’adar wasu aka yi.
Sa wando na daya daga cikin abubuwan da ke saka wasu ‘yan mata cikin halin kaka nikayi kamar su fyade da cin zarafi da sauran munanan yanayin da sukan sami kansu a wasu lokuta.
Saurari cikakkiya kirar.