Jerin wasu mutane nada ban haushi musamman a shafufukan yanar gizo, sau da yawa mutane sukan jama kansu kiyayya batare da la’akari da yadda sauran mutane suke ba. A dalilin ire-iren wadannan mutane ne shafufukan zumunta kamar su facebook suka samar da damar cire mutun a matsayin aboki.
Wasu daga cikin abubuwan da ke bama mutane haushi da wasu a shafufukan su, sun hada da yadda wasu kan canza hotunan su kamar sau 5 a rana, a dalilin haka mutun bai iya gane wannene mutumin gaskiya. Haka mutane da kan dauke basirar wani su maidata tasu, kamar yadda wasu kan sace yadda wasu ke rubutun irin abubuwan da suke so ko sukafi sha’awa.
Haka mutane da kan yi rubutu batare da sake duba rubutun su don duba wasu kurakurai don gyara kamun su saka a shafin su, da saka wasu hotuna da basu kamata ba, ko bidiyo. Haka da irin mutane dake bada labari daya fiye da sau daya. Kana masu daukar hotunan jikin su don nuna wani bangaren jikin su, suma irin wadannan mutane da dama basu son abokantaka dasu a shafufukan zumunta. Don haka matasa sai a kokarta wajen ganin an kiyaye yadda ake gudanar da mu'amalar yau da kullun musamman a shafufukan zumunta, ganin cewar wasu abokan ba'asan juna ba, don haka sai a kokarta ganin an gyara zumunci.