Tallafin nera biliyan biyu da gwamnatin tarayyar ta ba jihohin arewa maso gabas ya jawo tofin alla-tsine. Lokacin da yake mayarda martani a madadin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno,Gombe, Taraba da Yobe gwamna Nyako na jihar Adamawa ya ce abun takaici ne a ce an ba jihohin shida tallafin nera biliyan biyu kawai yayin da shugaban kasa ya ware ma jiharsa ta Bayelsa tallafin nera biliyan goma sha daya da sunan farfado da tattalin arziki. Cikin jihohin shida uku na karkashin dokar ta baci kuma suna fama da rashin zaman lafiya. Bayelsa bata fuskantar kowane irin matsala don haka tattalin arzikinta yana cigaba. Gwamna Nyako mai magana da yawun sauran gwamnonin ya ce shugaban ya je wani yankin kasar ya kashe biliyan dari biyu amma ya zo nasu yankin ya bayar da nera biliyan biyu kawai. Ya ce ina adalci a shirin? Ya ce shi shugaban kasa bai san yankin na cikin matsala ba ne? Su basu da haki ne? Ya ce sun zabi PDP to me suke samu illa ana cigaba da sasu cikin wahala.
Ga manazarta kan harkokin tattalin arziki da kasuwanci irin su Malam Mohammed Isma'il ya ce ba mamaki idan jihohin suka koka. Ya ce jihohi shida aka ba biliyan biyu to nawa kowace jiha zata samu? Kuma jihohin dake cikin dokar ta baci kamar jihar Adamawa su ne suke biyan kusan kashi saba'in na kudaden da ake kashewa kan jami'an tsaro a jihohinsu. To kudin da ake ikirarin an basu me zai yi masu? Ya ce a kwatanta kudin da nera biliyan goma sha daya da shugaban kasa ya ba jiharsa ko kuma nera biliyan uku da ya ba 'yan fim.Kwanan nan ana cewa zunzurutun kudi kamar tiriliyon takwas sun bace to yaya za'a ce an ba jihohi shida dake cikin matsaloli nera biliyan biyu kawai?
Wani na hannun daman tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo Chief Femi Fanikayode yana zargin cewa gwamnatin PDP karkashin Jonathan na son wargaza Najeriya. Da yake ganawa da manema labarai a Yola Chief Fanikayode yace muddin 'yan Najeriya basu tashi ba a zaben 2015 su hana Jonathan cigaba da mulki to kasar zata shiga wani mawuyacin hali. Idan har ba'a takawa Jonathan birki ba to fa shi da PDP zasu hallaka kasar. Zai yi anfani da duk karfin gwamnati ya kakkabe duk wadanda basu goyi bayansa ba.
Saidai kuma mukaraban shugaba Jonathan kaman su Ahmed Ali Gulak na ganin babu abun da zai hana shugaban kasar zarcewa. Gulak ya ce idan Allah ya tattara Najeriya ya ba Jonathan to duk wanda yake fada da Jonathan yana fada da Allah.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz