Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Nijar: Yau Mahaman Ousman Ke Gabatar Da Kara Da Hujjoji a Kotu


Dan takarar jam’iyar RDR Canji ya sanar cewa a yau din ne Alhaji Mahaman Ousman zai kai nasa koken don ganin kotun ta soke sakamakon wasu gundumomin da yake zargin an aikata ba daidai ba.

Sama da kuri’u dubu 900 ne kwamitin yakin neman zaben dan takarar ‘yan adawa Mahaman Ousman ke zargin an yi amfani da su wajen tafka magudi a zaben 21 ga watan Fabrairu wadanda kuma dan takarar zai gabatar da su a yau Litinin a gaban kotu a matsayin hujjoji.

Sakataren jam’iyyar RDR Canji Dr Sani Abdou wanda ya karanta wa manema labarai bayanan da suka tattara daga wannan yanki zuwa wancan ya fayyace irin barnar da kwamitin yakin zaben Mahaman ousman ya ce an tafka.

Tursasa wa wakilansu da bindiga a runhunan zabe da cika akwatuna da kuri’un karya tare da rubuta jabun rahoton karshen zabe na daga cikin abubuwan da kwamitin ke zargin sun faru a ranar 21 ga watan Fabrairu a wasu yankuna saboda haka yace Mahaman Ousman da abokan tafiyarsa na CAP 20 21 da ACC da FRC ba za su yarda a kwace masu galabar da suka samu a zaben nan ba.

A yau ne wa’adin shigar da korafi a gaban kotun tsarin mulki ke cika. A cewar darektan yakin neman zaben dan takarar RDR Canji Honorable Falke Bacharou sun kammala hada komai don gabatar da kokensu akan bukatar kotun ta soke sakamakon yankunan da irin wadanan abubuwa na asha suka wakana.

To sai dai a ta su sanarwar, jam’iyun kawancen Coalition Bazoum 2021 masu goyon bayan dan takarar PNDS Tarayya wanda hukumar zabe ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben 21 ga watan Fabrairun sun jaddada goyon bayansu a gare shi. Suna masu cewa basu da wata tantama a game da nasarar da ya samu saboda haka zuwa kotu ba zai daga masu hankali ba.

Nan gaba a cikin watan nan na Maris ne kotun tsarin mulkin kasa za ta bayar da sunan wanda zai gaji shugaba mai shirin barin gado Issouhou Mahamadou a tsakanin Bazoum Mohamed da Mahaman Ousman.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

XS
SM
MD
LG