Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Kotu Don Kalubalantar Sakamakon Zabe - Mahamane Ousman


Mahamane Ousman
Mahamane Ousman

Zabin da dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar RDR Tchanji Mahamane Ousmane ya yi, na shan yabo a wurin kungiyoyin kare mulkin dimokradiyya.

Wasu kungiyoyi masu rajin kare dimokaradiya a Jamhuriyar Nijar, sun yabawa dan takarar jam’iyar RDR Canji Alhaji Mahaman Ousman, saboda yadda ya zabi ya garzaya kotu domin ta bi masa kadin magudin da yake zargin an tafka a zaben 21 ga watan Fabrairu.

Maimakon ya bi hanyar tarzoma, suna masu jan hankulan ‘yan kasar ta Nijar su nisanci ‘yan siyasar dake furta kalamai irin na neman tashin hankali.

Tun bayan sanar da sakamakon wucin gadin da ya bayyana shi a matsayin wanda ya sha kaye a zagaye na 2, na zaben da ya hada shi da Bazoum Mohamed na jam’iyar PNDS, mai mulki dan takarar jam’iyar RDR Mahaman Ousman, ya yi watsi da wannan sakamakon wanda a take ya yanke shawarar kalubalantarsa a kotun tsarin mulkin kasa.

Ya kuma sha nanata wannan matsayi mafari kenan kungiyar CCDR ke yabawa wannan halayyan na sa. Siraji Issa na daga cikin jigo a kungiyar.

Yana mai cewa; A makon jiya wasu biranen kasar sun yi fama da tarzomar watsi da sakamakon zabe, yayin da Mahaman Ousamn, ke fadi yana kari cewa ya kudiri aniyar zuwa kotu, saboda haka kungiyar ta shawarci tsohon shugaban kasar ta Nijar ya yi watsi da shawarwarin mutanen da ta kira miyagun abokan tafiya.

A nan gaba cikin watan nan na Maris ne kotun tsarin mulkin kasa za ta bayyana sakamakon dindindin, na zaben shugaban kasa na 21 ga watan Fabrairu, da ya gabata dalili da yasa kungiyar CCDR a ta bakin shugabanta Issouhou Sidibe ke kiran ‘yan kasa su kasance masu nuna halin dattako da bin umurnin hukumomi domin tabbatar da zaman lafiya.

A yammacin Juma’ar da ta gabta ne wata tawagar ‘yan hamayya a karkashin jagorancin Mahaman Ousman ta ziyarci ofishin jam’iyar PJP Dubara, ta tsohon shugaban gwamnatin mulkin soja Janar Salou Djibo, sai dai ta yi kicibus da jami’an tsaron Garde Nationale da suka rufe kofar gidan ba shiga ba fita, sakamakon wani umurnin da suka ce yazo masu ne daga sama.

Ga rahoton da wakilin Muryar Amurka a Yamai Souley Moumouni Barma ya aiko muna.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG