Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN NIJAR: Yadda Aka Kammala Yaki Neman Zabe, CENI Mun Shirya Tsaf


Nijar
Nijar

Jiya aka rufe yakin neman zabe a Jamhuriyar Nijer bayan da kowane daga cikin ‘yan takarar biyu da zasu fafata a zabe ranar Lahadi 21 ga watan Fabrairu suka shafe makwanni kusan uku suna zagaya sassan kasar da nufin tallata manufofinsu a wajen talakawa. 

Jam’iyyar PNDS Tarayya da ke unguwar Zabarkun ta gudanar da yaki neman zaben ta na karshe a ranar Juma’a da daddare, inda magoya bayan jam’iyyun kawance na Coaliation Bazoum 2021 suka hallara, kafin a rufe yakin neman zaben a hukumance.

Jami’in kula da harakokin sadarwa a kwamitin yakin zaben dan takarar PNDS Tarayya, Tahirou Garka, ya ce sun gamsu da yadda jama’a ta karbi Bazoum Mohamed da tawagarsa a yayin zagayen da suka gudanar don tallata manufofin dan takarar abin da a fili ke nuna su zasu lashe wannan zabe.

Bazoum Mohamed
Bazoum Mohamed

Suma magoya bayan jam’iyyun kawance na CAP2021 masu ra’ayin Mahaman Ousman sun zagaya titunan birnin Yamai, inda suka kuma gudanar da kade-kade a ofishin jam’iyyar da ke dab da dandalin Place Toumo.

Shugabar matan RDR Canji, Aichatou Ibrahim, ta ce suna da kwarin gwiwa Mahaman Ousman ne zai lashe zaben na ranar Lahdi 21 ga watan Fabrairu, sakamakon lura da goyon bayan da ya samu daga wasu gaggan ‘yan siyasa da magoya bayansu.

NIGER: 'Yan adawana Jamhuriyar Nijar
NIGER: 'Yan adawana Jamhuriyar Nijar

Shi kuwa a nasa bangaren mataimakin shugaban hukumar zaben jamhuriyar Nijar ta CENI, Dr. Aladoua Amada, ya ce idan dai kana son kayi zabe a cikin rumfar da babu sunanka to dole ne ka samu wata takarda daga hukumar kafin a baka dama kayi zabe.

Ya kuma kara da cewa an takaita duk rumfar zaben kar ya wuce mutum 22, saboda hukumar zabe ta kare alhakin mutane kada ta bada dama ayi cuwa cuwar zabe.

Amma a jihar Tahoua bangarorin biyu da za su fafata sun ce sun shirya tsaf domin karawa a zaben shugaban kasar zagaye na biyu, inda suka yi kira da magoya bayansu da su fito kwansu da kwarkwatar su domin kada kuri’un su.

Wasu ‘yan Nijar sun yi fata cewa Allah yasa a yi wannan zaben lami lafiya, kana Allah ya basu wanda zai fitar da su daga talaucin da su ke ciki.

Kungiyoyin fararan hula masu saka ido a zabe sun ce sun shirya tsaf kawai suna jiran su ga yadda za ta kaya a zaben na ranar Lahadi.

Rumfunan Zabe sama da 25,000 ne aka yi tanadi domin baiwa jama’a damar sauke nauyin da ya rataya a kan su, saboda haka hukumar CENI ta sake nanata cewa da misalin karfe 8 na safe agogon Nijar ne za a bude rumfunan zabe wadanda ya kamata su rufe bayan sa’o’i 11 don fara kirga kuri’u a kan idon wakilan dukan ‘yan takarar biyu.

XS
SM
MD
LG