Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Zai Ziyarci Jihohi Masu Muhimmanci a Zaben Amurka


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya shirya ziyartar manyan jihohi hudu masu muhimmanci sosai a zabe a mako mai zuwa, a yayin da jam’iyyun Republican da Democrats ke shirin tarukan su na kasa.

Wata majiya ta kusa da masu tsara ziyarar ta ce Trump zai ya da zango a Minnesota, Wisconsin, Arizona da Pennsylvania, dukan su jihohi ne da ake sa ran suna da muhimmanci wajen fitar da zakara a zaben na ranar 3 ga watan Nuwamba.

‘Yan jam’iyyar Demokrats za su gudanar da babban taronsu mafi yawa ta hanyar sadarwar bidiyo a Milwaukee ta jihar Wisconsin a mako mai zuwa. Mujallar Milwaukee Sentinel ta ce Trump na duba yiwuwar gudanar da gangamin yakin neman zabensa a Oshkosh ta jihar Wisconsin.

Trump da ke fafutukar tunkarar annobar coronavirus da komadar tattalin arziki, na duba hanyoyin da zai iya yin nasara akan Biden, bayan da dan takarar na jam’iyyar Demokrats ya zabi ‘yar majalisar dattawa daga Carlifornia Kamala Haris a matsayin mataimakiyarsa a zaben.

Shugaban mai ci yanzu da ke neman tazarce a wa’adin mulki na 2 na shekaru 4, shi ne ke bayan Biden a zabukan jin ra’ayoyin jama’a da dama a matakain kasa da na jihohi, duk kuwa da cewa Trump ya nace akan shi ke kan gaba.

Akwai yiwuwar ziyarar ta Trump a mako mai zuwa ta kumshi hadin gwiwar jami’an fadar shugaban kasa ta White House da kuma na gangamin yakin neman zabensa. Majiyar ta ce yana kudurin yada zango a garin Biden na Scranton na jihar Pennsylvania.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG