Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Na Fuskantar Caccaka Kan Batun Haraji


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Bayan kusan shekaru hudu da dan takaran shugaban kasa a waccan lokaci Donald Trump ya fuskanci tambayoyi a kan biyan haraji yayin wata mahawara da aka yayata a telbijin kasa baki daya

Wannan batu ya sake tasowa a zaben shekarar 2020, a daidai lokacin da Trump da abokin karawarsa Biden ke shirin yin mahawara da yammacin yau Talata.

Jaridar New York Times ta buga dalla dalla a shafinta na yanar gizo cikakken bayani a kan biyan harajin Trump na shekaru 20, da shugaban ya gaza bayyanawa tun da farko da ya kaddamar da gangamin yakin neman zabe a shekarar 2015.

Da aka yi masa tambaya a kan wannan batu, Trump ya kira labarin da cewa kanzon kurege ne.

Jaridar Times ta ce bayanan biyan haraji da take nazari a kai ta same shi ne daga wani tushi da doka ta amince da shi, a dan haka wani abu ne da za a iya tantancewa idan aka kwatanta da bayanan dake bainin jama’a da ma na sirri da ta samu a baya.

Jaridar New York Times ta ce ta sake duban bayanan biyan harajin Trump wanda ya nuna ya kwashe shekara da shekaru baya biyan haraji, inda galibi yake ayyana asara fiye da kudaden shige da yake samu a wadannan shekaru.

Bayanan biyan haraji ba na bainin jama’a bane, amma tun zamanin shugabancin Richard Nixon, ‘yan takara bisa son ran su suke bayyana bayanan kudaden su domin amsa duk wasu tambayoyi da kuma magance batun yiwuwar aikata son kai.

Amma ga dukkan alamu shugaba Donald Trump ya yanke wannan al’ada a lokacin yakin neman zaben shekarar 2016 kana ya fada a waccan lokaci cewa bayanan harajin sa batu ne na hukumar IRS mai tattara haraji, dan haka ba zai iya bayyana su ba, sai dai ya yi alkawarin yin hakan idan an bashi dama.

Abokin karawar Trump Biden bai yi wani jawabi a fili ba game da batun harajin Trump na ranar Lahadi, amma kamar ‘yar takarar Democrat a zaben shekarar 2016, Hilary Clinton, tsohon mataimakin shugaban kasar ya kalubalanci Trump da ya bayyana biyan harajin sa ga jama’a.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG