Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Kada Kuri'arsa a Zaben Shugaban Kasa


Shugaba Trump Bayan da ya kara kuri'arsa.
Shugaba Trump Bayan da ya kara kuri'arsa.

Shugaban Amurka Donald Trump da ke takara karkashin jam’iyyar Republican, ya kada kuri’arsa a Florida a zaben shugaban kasa da za a yi na ranar uku ga watan Nuwamba.

Hakan na faruwa ne a radar Asabar yayin da abokin hamayyarsa na Jam’iyyar Democrat Joe Biden ya kwashe yinin, hankalinsa na kan jihar Pennsylvania da ta kasance mai matukar muhimmanci a wannan zaben.

Trump, wanda ya koma da zama a jihar ta Florida daga New York a bara, ya kada kuri’ar tasa ne da safiyar yau a yankin West Palm Beach bayan da ya kwana a gidan shakatawarsa na Mar-a-Lago da ba shi da nisa da wurin.

Bayan kada kuri’arsa, da aka tambaye shi wa ya zaba sai ya ce, “na zabi wani mutum ne da ake kira Trump.”

Shugaban na Amurka na kan hanyarsa ne ta zuwa Lumberton da ke jihar North Carolina inda zai gudanar da gangamin yakin neman zabe. Zai kuma gudanar da makamantan wadannan gangami ma a Circleville da ke jihar Ohio da kuma Waukesha da ke jihar Winsconsin.

Shi kuwa tsohon mataimakin shugaban kasar Biden na gudanar da na shi taron ne a karamar hukumar da ake kira Bucks County ta hanyar ratsawa da motoci, wacce ke wajen Philadelphia, wacce kuma Hillary Clinton ta lashe da ‘yar karamar tazara a shekarar 2016 da kuma wata karamar hukuma da ake kira Luzerne.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG