Shugabanni biyu, Fatai Ayoola, na karamar hukumar Ajeromi Ifelodun da Emmanuel Bamgboye, na karamar hukumar Mushin, su ne suka bayyana hakan bayan kada kuri’a a Legas ranar Asabar.
Ayoola ya lura cewa jami’an INEC a rumfunan zabe sun fi saurin amfani da na’urar sabanin lokacin zaben shugaban kasa.
“A kan batun BVAS, na ga yanzu mutane sun saba da shi sabanin lokacin zaben shugaban kasa da har yanzu wasu daga cikin jami’an wucin gadi ba su san na’urar ba,” inji shi
Ayoola ya ce rahotannin da aka samu daga sassa daban-daban da kuma gundumomi sun nuna cewa masu zabe sun yi zabe tare da gudanar da kansu cikin tsari.
Ya ce babu wani nau’i na cin zarafi daga kowa domin duk jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda sun kewaye don tabbatar da cewa aikin ba su da matsala.
A nasa bangaren, Bamgboye ya ce INEC ta cika alkawarin da ta dauka na inganta harkokin zabe ta hanyar inganta BVAS.
"Ayyukan BVAS ya inganta ainun idan aka kwatanta da yanda abubuwa suka faru a baya.
“A dukkan mataki, muna ganin ci gaba lokaci lokaci kuma dimokuradiyyarmu za ta fi dacewa da ita. Za mu iya cewa mun sami ingantaccen aikin BVAS.
"Kwanciyar hankali da zaman lafiya da muka gani a wannan zabe ya samo asali ne daga BVAS," in ji shi.
Bamigboye ya ce BVAS ya taimaka wajen cire satar tantance masu kada kuri’a sabanin a baya lokacin da za su iya karbar katin zabe na wasu mutane don kada kuri’a.
-The Guardian