A Najeriya, siyasar ubangida na tasiri matuka ga sha’anin zabe musamman na fidda gwani, amma Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa masanin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero da ke Kano, yace ko da yake a jamhuriya ta daya akwai yanayi ko tsarin siyasar ubangida a Najeriya, amma ba irin na yanzu ba ne. Kamarsu Malam Aminu Kano da Sardaunan Sokoto, da duka iyaye na siyasa sukan bada umarni a bi, amma sun tafiyar da jagoranci bisa akida da nusar da magoya baya.
To amma a cewar, Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa, tsohon wakilin mazabar Kano ta kudu a majalisar dattawan Najeriya, gwamnonin kasar su ne tushen matsalar siyasar ubangida, yana mai cewa sun dakile ci gaban dimokaradiyya a Najeriya ta hanyar makure wuyan kananan hukumomi da majalisun dokoki na jihohinsu.
"Ba sa bari harkokin mulki su gudana a kananan hukumomi, ba sa barin ‘yan majalisar dokoki su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, kuma basa bari a yi zaben cikin gida na jam’iyyu bisa ka’idar zabe, sai dai suyi abin da ake kira dauki dora a yayin fitar da ‘yan takara," a cewar Doguwa.
Watakila hakan ne ya sa masana kimiyyar siyasa ke cewa akwai alaka ta kud-da-kud tsakanin siyasar ubangida da siyasar kudi wadda kan rikide ta haifar da yanayin amfani da kayayyakin masarufi domin jan hankalin masu zabe.
Sai dai ana ci gaba da mahawara a tsakanin manazarta kan cewa ta yuwu sauya fasalin wasu daga cikin takardun kudin Najeriya ka iya tasiri ta wannan fuska, amma Dr. Dukawa ya ce sauya fasalin takardun kudin ka iya rage amfani da kudi a zabe, amma akwai rahotannin da ke cewa ‘yan siyasa sun yi amfani da kayayyakin masarufi domin raba wa masu zabe.
Masana ilimin kimiyyar siyasa sun ce sayen kuri’a karkashin tsarin siyasar ubangida na nufin tafka magudin zabe.
Shin ko gwamnoni kan taka rawa a nan? Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa ya ce gwamnoni ke daure gindin siyasar kudi a Najeriya, domin kuwa kusan dukkanin arzikin kasa na hannunsu.
A zaben shugaban kasa dai hukumar zaben Najeriya ta INEC ta yi amfani da na’urar BVAS a matsayin daya daga cikin matakan kawar da magudin zabe a kasar, sai dai jam'iyyun adawa da wasu 'yan Najeriya su koka kan kurakuran da aka fuskanta wajen amfani da na'urar.
Wannan ya sa hukumar INEC dage zaben gwamnoni da na 'yan majalisar jiha zuwa Asabar 18 ga watan Maris don samun damar saita na'urar ta BVAS.
Saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari: