Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben 2023: 'Yan Adawa Sun Kara Kaimi A Yakin Neman Zabe A Inda Gwamnoni Ke Kammala Wa'adin Su


Wata rumfar zabe a jihar Anambra (Facebook/ INEC)
Wata rumfar zabe a jihar Anambra (Facebook/ INEC)

Duk da ba lalle ba ne gwamnoni da ke mulki su lashe zabe karo na biyu, amma kwarin guiwar ‘yan hamaiya ya fi karfi a jihohin da gwamnaonin za su kammala wa’adi a ranar 29 ga watan mayu mai zuwa.

A akasarin shiyyoyin siyasa na Najeriya 6 akwai irin jihohin da gwamnonin su ba sa cikin takarar.

Wasu daga jihohin da lamarin ya shafa sun hada da Kano a arewa maso yamma, Ribas a kudu maso kudu, Abia a kudu maso gabar, Filato a arewa ta tsakiya, Ekiti a kudu maso yamma da Taraba a arewa maso gabar.

In an duba wani abin lura dukkan gwamnonin arewa maso yamma 7 in ka debe jihar Zamfara za su kammala wa’adi a wannan karo inda a arewa maso gabar duk gwamnonin 6 in ka debe Taraba na neman tazarce karo na biyu.

Bambancin arewa ta tsakiya nan ma jihar daya ce wato Kwara gwamnanta ke neman wa’adi na biyu amma ita jihar Kogi da ba ta cikin zaben gama-gari sai sharhin ya zama na daban.

Jami’in kamfen na jam’iyyar adawa ta NNPP a jihar Taraba Injiniya Ahmed Zakari Nguroje, na fifita dora kamfen din kan yaki da bambance-bambancen addini da kabilanci a matsayin mafita ga kowace jam’iyya a jihar.

Shi ma kakakin kamfen na babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Katsina Imran Wada Nas na cewa duk da jihar ta shugaba Buhari ce amma wannan karo sun shirya kawo sauyi.

Hukumar zaben Najeriya INEC da ke shirin gudanar da zaben a ranar Asabar din nan mai zuwa, ta ba wa jam’iyyu damar cigaba da kamfen har rana wayewar jajiberin zaben.

Zainab Aminu jami’a ce a sashen labarun hukumar da ke cewa ‘yan takara ka iya kamfen har ranar Alhamis din nan.

Ana jiran bayani a hukumance daga hukumar ta INEC kan kammala saita na’urorin BVAS don gudanar da zaben da za a iya samun shaida ga korafe-korafen da kan taso a bayan zabe.

Ga dai sautin rahoton Nasiru Adamu El Hikaya daga Abuja:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

XS
SM
MD
LG