Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben 2023: An Gargadi Ma'aikatan Zabe A Cross River Da Su Guji Shirya Magudi A Zaben Gwamnoni Na Yau Asabar


Shugaban hukumar zabe ta INEC Farfesa Yakubu Mahmood
Shugaban hukumar zabe ta INEC Farfesa Yakubu Mahmood

Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta, (INEC) a Cross River a ranar Juma’a ta yi barazanar ladabtar da jami’an tattara sakamako da malaman zabe da suka yi magudi wurin gudanar da zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha.

Farfesa Gabriel Yomere, Kwamishinan Zabe na INEC na Cross River ne ya yi wannan barazanar a lokacin horar da ma’aikatan wucin gadi na hukumar a Calaba da za su gudanar da zaben ranar 18 ga Maris a Cross River.

Yomere ya bukaci jami’an da su kasance masu zaman kansu ba tare da karkata wani bangare ba wajen gudanar da ayyukansu tare da kaucewa duk wani laifi.

Wata rumfar zabe a jihar Anambra (Facebook/ INEC)
Wata rumfar zabe a jihar Anambra (Facebook/ INEC)

Wakilin INEC na jihar, ya shawarci ma’aikatan da su dauki horon da muhimmanci kuma su guji duk wani nau’i na sauya takardar sakamako.

Ya kuma sanar da duk ma’aikatan wucin gadin da masu ruwa da tsaki cewa babu daya daga cikinsu da ke da hurumin sauya zaben ya kara da cewa hukumar za ta gurfanar da duk wanda ya nemi tauye sahihancin zaben da gangan gaban kotu.

“Don kauce wa shakku, sashe na 120 na dokar zabe ta 2022 ya bayyana cewa jami’an da ke aikin zabe ba tare da wani uzuri na doka ba suka aikata ko kuma suka yi watsi da aikin da suka yi rantsuwar zasu yi adalci, za a gurfanar da su a gaban kuliya kuma idan aka same su da laifi za a daure su gidan yari.

INEC
INEC

“Lokacin zaman gidan yari yana kamawa ne daga shekaru uku na jami’an tattara bayanai da kuma watanni 12 ga shugabannin jami’an da sauran ma’aikatan zabe, ciki har da cin tara idan bukatar hakan ta taso.

“Wannan sashe ya kuma shafi duk wani mutum, jam’iyyun siyasa ko wakilan jam’iyyarsu da suka hada baki wajen bayyana sakamako na karya ko buga wani sakamakon da bai wuce wanda hukumar ta sanar ba,” inji shi.

Haka kuma Wakilin INEC ya yi kira ga wadanda suka cancanci kada kuri’a da su fito sosai cikin tsari tare da kada kuri’unsu a zaben na ranar Asabar.

XS
SM
MD
LG