Hukumar INEC dai ta dage lokacin zaben na gwamnoni da mako guda zuwa yau Asabar. Za a gudanar da zabukan ne a jihohi 28, yayin da sauran jihohi 8 na kasar lokacin zabensu dabam da sauran, sakamakon hukuncin kotu a baya da ya sauya lokutan zabensu.
Akalla manyan jam’iyyun APC da PDP na da ‘yan takara a dukkan jihohi inda wasu jam’iyyu da suka hada da NNPP, Labour, SDP, YPP da sauransu suka tsayar da nasu ‘yan takarar da dama.
Tun a zanga-zangar da ‘yan adawa suka yi zuwa hukumar INEC kan cewa BVAS ba ta yi aiki ba a zaben shugaban kasa, INEC a ta bakin jami’a a sashen yada labaran hukumar Zainab Aminu, ta nanata batun shirin aiki da BVAS a zaben na yau.
Da karfe 2.30 na ranar Asabar agogon Najeriya za a rufe rumfunan zabe, amma duk wanda ke kan layi zai samu damar kada kuri’a ko karfe nawa hakan zai dauka.
Saurari rahoton Nasiru Adamu Elhikaya: