Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Koli Ta Kori Kara Kan Bukatar Soke Cancantar Takarar Tinubu


Shugaban APC Bola Tinubu
Shugaban APC Bola Tinubu

Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da karar da wasu ‘yan jam’iyyar APC uku su ka shigar a gabanta, dake neman hana cancantar zababben shugaban kasa, Bola Tinubu takara, inda suka ce bai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata ba.

A wani hukunci da aka yanke a ranar 29 ga Maris, ta ce wadanda suka shigar da kara karkashin jagorancin Memuna Suleiman, ba su da hurumin shigar da karar a gaban babbar kotun tarayya.

Lokacin da aka kira karar, masu shari’ar biyar na Kotun Koli sun lura cewa wadanda suka shigar da karar, ba ‘yan takarar fidda gwani bane a jami’iyar APC, a don haka ba za su iya kalubalantar zaben Tinubu ba.

Da kotun ta lura da haka, lauyan wadanda suka shigar da kara ya nemi janye karar, inda kotun ta yi watsi da shi.

Kotun ta tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a ranar 17 ga watan Fabrairu.

Sun roki kotun da a cikin sauran bukatun su, ta ayyana Tinubu a matsayin wanda bai cika sharadin mafi karancin ilimi ba don tsayawa takarar shugaban kasa a Tarayyar Najeriya.

Sun bukaci kotun da ta bayar da umarnin haramtawa Tinubu tsayawa takara a jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa da za aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Masu shigar da karar dai sun kuma nemi umarnin hana Tinubu bayyana kansa a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da kuma yin umarni ga INEC da kada ta amince da Tinubu a matsayin dan takarar APC.

A wani hukunci da ya yanke a watan Nuwamba 2022, Mai shari’a Ahmed Mohammed na babbar kotun tarayya ya ce wadanda suka shigar da karar sun yi kuskure wajen daukar mataki kuma ba su da hurumin kafawa da kuma ci gaba da daukar matakin a kan APC.

Mai shari’a Mohammed, bayan da ya ce wadanda suka shigar da kara, wadanda ba ‘yan takarar jam’iyyar APC ba ne, ba su da wani katabus, kotun ta yi watsi da karar da cewa ba su da cancanta.

A kan daukaka kara, kotun daukaka kara a hukuncin da ta yanke a ranar 17 ga Fabrairu, 2023 ta yarda da rashin amincewar wadanda ake kara tare da soke bukatar daukaka karar da Suleiman da sauran su suka shigar.

Kotun, yayin da take yanke hukuncin daukaka karar, ta fada a cikin saurn batutuwa cewa, karar ba ta da wata kwakkwarar hujja kuma ta yi watsi da shi.

Kotun daukaka karar ce ta yanke hukunci ranar 17 ga watan Fabrairu, kotun kolin ta tabbatar da hukuncin da ta yanke a ranar 29 ga Maris.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG