Wani jami’in Amurka ya ce mai yiwuwa jerin takunkumin su fara aiki daga ranar Litini.
Firayim Ministan Ukraine Arseny Yetsenyuk ya zargi Rasha da kulle-kullen mamaye Ukrain ta fuska soji da kuma siyasa, a daidai lokacin da Ukraine din da Rasha ke ta girke sojoji daura da kan iyakan juna. Mr. Yetsenyuk ya gaya ma taron ministocinsa cewa Rasha so ta ke ta takalo yakin duniya na uku.
A halin da ake kuma, wani jami’in sojin Amurka ya fadi jiya Jumma’a cewa jirghin yakin Rasha ya shiga sararin saman Ukraine sau da dama cikin wasu sa’o’i 24 da su ka gabata.
Wani kakakin Ma’aikatar Tsaron Amurka ya yui kira ga Rasha da ta dau matakan kwantar da kurar.
A wani al’amarin kuma, wasu ‘yan aware magoya bayan Rasha a gabashin Ukarine sun kama tawagar sa ido kan harkokin soji ta kasa da kasa a jiya Jumma’a. ‘Yan a waren sun kame wata motar bus nai dauke da dinbin jami’an na kungiyar da ke Vienna ta hadin kai game da batun tsaro a Turai (OSCE a takaice) a kusa da garin Slovyansk.
Wakilin Rasha a kungiyar ta OSCE ya fadi yau Asabar cewa Rasha za ta dau dukkannin matakan da za ta iya daukawa wajen ganin san sako jami’an na sa ido.