NATO ta Nuna Yawan Sojojin Rasha Akan Iyakar Kasar Ukraine
NATO ta Nuna Yawan Sojojin Rasha Akan Iyakar Kasar Ukraine
NATO ta fitar da hotunan da tauraron dan adam ya dauka wanda suka nuna yadda sojojin Rasha suka taru akan iyakar kasar Ukraine.
WASHINGTON, DC —
Kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta gabatar da wasu hotuna da tauraron dan Adama ya dauka, da suka nuna abubuwan data ce sojojin Rasha ne suka taru kusa da kan iyakar kasar Ukraine, tare da tankokin yaki da jiragen saman yaki da kuma wasu kayayyakin, suna jiran umarni daga birnin Moscow.
Hotunan da aka gabatarwa kafofi yada labaru a jiya Alhamis, ya biyo bayan tabbacin da Rasha tayi ta nanata bayarwa cewa, bai kamata tura sojojin yasa a tada hankali ba
Kungiyar NATO ta gabatar da hotunan ne a yayinda gwamnatin Ukraine ke kokarin magance zaman tankiya a gabashin kasar, inda masu zanga zanga, wadanda suke goyon bayan Rasha suka mamaye gine gine a farkon wannan makon, suka gabatar da bukatun cewa a barsu su jefa kuri'ar hadewa da taraiyar Rasha.
Fadar shugaban Amirka ta White House tace a jiya Alhamis shugaba Obama ya tuntunbi shugabar Jamus Angela Merkel, kuma dukkan shugabanin sun sake yin kira ga kasar Rasha data janye sojojinta daga yankunan kan iyaka.