Jiya Litinin wani mai magana da yawun fadar shugaban Amirka ya fadawa 'yan jarida cewa gwamnatin Obama ta bukaci kasar Rasha data daina yin shishigi a gabashin kasar Ukraine, kuma tayi barazanar cewa idan Rasha tayi kunen kashi ga wannan bukata, to zata aza mata karin takunkunmi.
Shima sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry, a jiya Litinin ya zanta da takwaran aikinsa na Rasha Sergei Lavrov, a tattaunawar baya bayan nan daga cikin shawarwarin da suke yi akan al'amari kasar Ukraine.
John Kerry ya bukaci Rasha data fito filli tayi Allah wadai da aiyukan masu neman balewa a zaman masu yin zagon kasa da kuma tsokanar fada.
Ma'aikatar tsaron Amirka da ake cewa Pentagon ta tabbatar cewa jiragen ruwan yakin Amirka sun doshi tekun Bahar Asuwad domin marawa kawayenta na turai da suke yankin