Hague din yace sojoji dan kadan kawai aka janye daga cikin tarin sojojin da Rasha ta lafta bakin iyakar Ukraine, wanda hakan yake kawo zaman dar-dar, saboda ana tunanin wata zata iya abkawa Ukraine.
Kashashen Turai sun riga sun sakawa Rashan nasu takunkuman, saboda hadewarta da yankin Kirimiya, lamarin da Amurka ta kawayenta suka yiwa kafar ungulu.
Rasha dai ta shiga cikin wannan tsuburi a watan daya wuce, bayan hambare shugaban Ukraine Viktor Yanukovych wanda Rashan take goyawa baya. An hambare shine bayan share makonni jama’a suna zanga-zanga.