Shugaban Amurka Barack Obama shima ya soki abunda ya kira cigaba da dagula lamura a gabashin Ukraine, wajenda ‘yan aware masu goyon bayan Rashe dake dauke da makamai suka mamaye ofisoshin gwamnati.
Da yake magana a birnin Seoul dake Koriya ta Kudu, Mr. Obama yace zai tattauna da muhimman shuwagabannin Turai a yammacin yau Juma’a, akan karawa Rasha takunkunmi, idan har Rashan ta cigaba da irin wadannan halaye nata a Ukraine.
Shugaba Obaman ya kara da cewa dole ne Shugaba Vladimir Putin ya yanke shawara idan yanaso ya ga tattalin arzikin kasarshi mara karfi ya kara lalacewa, saboda yaki bin hanyoyin diflomasiyya wajen warware takkadamar Ukraine.
Kalaman nashi sun zo bai daya ne dana sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, wanda jiya Alhamis shima yace Moscow na jefa kanta cikin wata matsala mai tsada, saboda ta ki ta dakatar da ‘yan aware.