A wancan lokacin gwamnatoci sun taru a jihar Sokoto kuma sun dauki alkawarin ganin kasuwar ta tabbata amma hakan bai faru ba. To amma yanzu a kokarinta na bunkasa tattalin arziki gwamnatin Sokoto karkshin shugabancin Aliyu Magatakarda Wamako ta yi alkawarin gina kasuwar nan da shekaru biyu.
A mataki na farko gwamnatin jihar ta rabtaba hannu kan jarjejeniyar gina kasuwar tare da gudanar da ita tare da Hukumar Bunkasa Kasuwanci Da Kudade Ta Kasa Da Kasa wato IBFC a takaice. Hukumar ce zata samarda kudaden gina kasuwar wadda zata ci kudi dalar Amurka miliyan dari biyu da goma sha biyu ko nera miliyan dubu talatin da hudu.
Alhaji Aliyu Shehu Acida kwamishanan ciniki da masana'antu da yawon bude ido na jihar Sokoto shi ya wakilci gwamnan jihar a wurin kaddamar da aikin kasuwar. Ya ce idan aka gama kasuwar zata habaka tattalin arzikin Sokoto domin zata kawo masu kasuwanci daga jihohi da wasu kasashen duniya. Ya ce domin tabbatar da kasuwar gwamnati ita ta bada filin ginata ita kuma zata tanadi tsaro.
To ko menene ya ba hukumar IBFC karfin zuba kudi masu yawa a kasuwar, shugaban hukumar a Najeriya Dr. Husain Ali Boni Al Banao ya ce gina kasuwa a wurin da zai anfani jihohi uku ko hudu da kasashen duniya hudu ko fiye abu ne Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ta kasa yi. Kasuwar zata habaka tattalin arziki da cudanya da karfafa zamantakewa.
Hukumar IBFC ce zata samarda kudaden gina kasuwar ta kuma gudanar da ita na tsawon shekaru bakwai kafi ta mikawa gwamnatin Sokoto.
Ga karin bayani.