Sheikh Dahiru Bauchi ya ce 'yan majalisar dokokin Najeriya su kiyayi kan su da kafa dokar kayyade shekarun aurar da 'ya'ya mata
WASHINGTON, DC —
Shahararren Shehun Malamin Addinin Islama na Najeriya kuma jagoran Darikar Tijjaniya a Afrika ta yamma,Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya gargadi yan majalisar dokokin kasar Najeriya da kada su kafa dokar hana aurar da yarinya da ba ta cika shekaru goma sha takwas da haihuwa ba. Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce su yi hattara kuma ba su da hurumin yin haka. Sheikh Dahiru Usman Bauchi yayi wannan bayani ne a wata hirar da yayi da manema labarai a garin Bauchi. Wakilin Sashen Hausa a Bauchi Abdulwahab Mohammed ya halarci taron kuma ya aiko da rahoto.