Hukumar kula da ruwa da dukkan kogunan Najeriya (NIHSA) ta bayyana shirin fadada madatsun ruwa musamman da ke daf da birane don rage ambaliyar ruwa a Najeriya.
Shugaban hukumarNIHSA, Umar Ibrahim Muhammed wanda ya duba dam din da ya malale Maiduguri ya ce ya baza ma’aikatansa a dukkan fadin Najeriya don duba koguna da rubuta rahoton halin da su ke ciki.
“Yanzu haka duk ma’aikatana sun tashi su na nan haikan wanda muna tsammanin a cikin wannan satin da za mu shiga Insha Allahu kowanensu zai gabatar da sakamakon binciken da suke kan yi yanzu”
Umar Muhammad ya kara da cewa za a rage karfin ruwan wasu koguna ta hanyar bunkasa noman rani da gina wasu kananan madatsun ruwan da za a rika tura ruwan kogin da ke neman tumbatsa.
Game da madatsar ruwan da ta haddasa ambaliya a Maiduguri, Umar ya ce ruwan ne ya fi karfin madatsar kuma tushensa daga tsaunukan Mandara ne a kan iyakar Najeriya da Kamaru.
Masanin kimiyyar siyasar tattalin arziki na jami’ar Abuja, Dr.Farouk BB Farouk, ya aza alhakin ambaliyar ta Borno da sakaci da kuma rashin daukar matakai a baya ga wadanda kan yi sako-sako da alhakin da ke wuyansu.
Duk shekarar da a ka samu yawan ruwan sama, akan samu ambaliya a sassan Najeriya da kan faru bisa wasu dalilan ma da su ka hada da sauyin yanayi sanadiyyar hayaki da ke gurbata muhalli, sare bishiyoyi, toshe magudanan ruwa da gina gidaje kan kwazazzaban da ruwan damuna ke bi.
A saurari rahoton NAsiru Adamu El-hikata:
Dandalin Mu Tattauna