Gwamnan ya kuma tabbbatar da cewa mutane fiye miliyan 1 ambaliyar ya raba da gidajensu a birnin Maiduguri, fadar gwamnatin jihar Borno
Da yake bada gudunmowar kudi ga mutanen da suka rasa muhallansu dake neman mafaka a sansanin ‘yan gudun hiijira na Bakassi dake kan hanyar Biu zuwa Damboa a birnin Maiduguri, Zulum ya bayyana cewar za’a samar da abinci da sauran kayayyakin bukata, sannan an dauki ‘yan kwangilar da zasu rika ciyar da ‘yan gudun hijirar dake zaune a sansanin.
Gwamnan ya kuma bayyana daukar matakai masu dogon zango, inda gwamnati zata kafa kwamitin lafiya da zai yi nazarin yiyuwar barkewar cututtuka domin dakile illoli da yaduwarsu.
Ya kuma kara da cewar an fara gudanar da aikin nema da ceton mutanen da suka bata a yankunan da ambaliyar ta malale domin tantance asarar rayuka, a yayin da ake gaggauta tattara bayanan wadanda al’amarin ya shafa.
Game da musabbabin afkuwar ambaliyar, gwamnan ya dora alhakin hakan akan mamakon ruwan saman da ake samu a daminar bana.
Dandalin Mu Tattauna