Tinubu ya bada umarnin ne a cikin sanarwar da mashawarcinsa na musamman akan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ya fitar a yau Talata, inda ya bayyana tsananin damuwa game da ambaliyar.
Ambaliyar ruwa mafi muni da aka gani cikin gomman shekarun baya-bayan nan ta raba dubban mazauna yankin da muhallansu tare da shafar muhimman gine-gine irinsu gidan waya da asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri.
Sanarwar ta kuma mika sakon ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar jihar, musamman iyalan da suka yi asarar sana’o’insu sakamakon ibtila’in da tumbatsar da madatsar ruwa ta alau ta jawo.
A yayin da hukumomin da al’amarin ya shafa ke cigaba da tantance irin barnar da ambaliyar ta haddasa, Shugaba Tinubu ya bukaci a gaggauta kwashe mutane daga yankunan da ruwa ya malale.
Ya kuma baiwa Gwamna Babagana Zulum tabbacin cewa a shirye gwamnatin tarayya take tayi hadin gwiwa domin samar da bukatun bada agajin gaggawa na al’ummar da ambaliyar ta shafa.
Haka kuma, shugaban kasar yace zai cigaba da jajircewa wajen samar da kudade daga asusun tarayya domin tallafawa jihar a wannan mawuyacin hali.
Dandalin Mu Tattauna