Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihohi 15 Na Amurka Sun Kada Kuri'a A Gagarumin Zaben Fidda Gwani Na Shugaban Kasa


Joe Biden da Shugaban Kasar Amurka Donald Trump.
Joe Biden da Shugaban Kasar Amurka Donald Trump.

Miliyoyin Amurkawa a jihohi 15 da tsibirin Samoa na Amurka ne ke kada kuri'a a yau Talata, rana mafi girma ta kada kuri'a a zaben 'yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Democrat da Republican.

Sakamakon farko ya nuna shugaba Joe Biden da tsohon shugaban kasa Donald Trump sun lashe gasar jam'iyyunsu a Virginia, North Carolina, Maine, Oklahoma, Tennessee da Alabama. Biden kuma ya lashe Vermont da Massachusetts. Har yanzu ba a bayyana na bangaren Republican ba a jahohin biyu.

Sai dai daga Biden har Trump babu ko dayansu da zai iya nasarar zama dan takarar a shugaban kasa na jam’iyyarsa zaben na yau Talata.

Super Tuesday primary election in McAllen
Super Tuesday primary election in McAllen

Amma dayake sama da kashi uku na wakilai a manyan tarukan jam'iyyun na wannan bazara ake zawarci, da Biden da Trump kowannensu na iya daukar wani babban mataki don samun nasarar cin mafi yawan wakilan babban taron, kuma nan ba da jimawa ba za su iya nasarar zama ‘yan takarar jam'iyyar a zabukan fidda gwani masu zuwa nan da makonni masu zuwa.

Biden bai fuskanci wani kalubale sosai ba a takarar Democrat, yayin da Trump ke da abokiyar hamayya daya kawai da ta rage, wato tsohuwar jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley.

Trump dai ya doke ta a kowace fafatawa a zaben fidda gwani na jahohi ko da yake kawo yanzu, Haley ce ta yi nasara a ranar Lahadin da ta gabata a birnin Washington, D.C., inda ‘yan jam’iyyar Republican 2,000 suka fito don kada kuri’a a babban birnin, inda jam’iyyar Democrat ke da rinjaye. Ita ce mace ta farko da ta taba lashe zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG