Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Ya Caccaki Trump Yayin Jawabinsa Na Shekara-shekara


Shugaban Amurka, Joe Biden ya bude jawabinsa na shekara-shekara tare da sukar Trump kai tsaye kan gayyatar Shugaban Rasha Vladimir Putin da ya kai wa sauran kasashen kungiyar NATO hari idan ba su kashe kudi mai yawa kan tsaro ba.

Shugaba Biden ya yi jawabin ne a wani zama na hadin gwiwa na Majalisar Wakilai da Majalisar Dattijai da ake gudanarwa shekara-shekara a Amurka kan halin da kasa ke ciki.

Shugaba Biden ya kuma bayyana cewa, gwamnati za ta yi kokari ta dawo da Amurkawan da Rasha ke tsare da su.

"Za kuma mu yi aiki ba dare ba rana don dawo da Evan da Paul gida, Amurkawan da Rasha ke tsare da su ba bisa ka'ida ba."

Shugaban ya bayyana nasarorin da ya samu kan ababen more rayuwa da masana'antu, ya kuma matsawa Majalisa ta amince da karin taimakon makamai ga Ukraine, da tsauraran ka'idojin shige da fice da rage farashin magunguna.

Ya kuma tunatar da masu kada kuri’a halin da ya gada a lokacin da ya shiga ofis a shekarar 2021 a yayin da ake cikin bala’in annoba da tattalin arziki. Yana mai nuni da yadda kasar ta farfado bayan barkewar annobar.

"Jama'a, na gaji tattalin arzikin da ya karye," Inji Biden.

Ya kara da cewa, "Yanzu tattalin arzikinmu ya zama abin sha’awa a kasashen duniya a baki daya. An sami sabbin ayyuka miliyan goma sha biyar a cikin shekaru uku kawai. Rashin aikin yi ya yi kasa kwarai."

Biden ya gargadi Isra'ila da cewa ba za ta iya amfani da agaji a matsayin wani "ciniki" ba yayin da ya yi kira da a gaggauta tsagaita bude wuta na wucin gadi da Hamas a mummunar yakin Gaza.

Biden yace, "Ga shugabanin Isra'ila, abun da zan fadi shi ne- Taimakon jinkai ba zai zama abin la'akari na yin sulhu ba. Karewa da ceton rayukan marasa laifi dole ne ya zama fifiko," in ji Biden

Ya kara da cewa Isra'ila na da hujjar kaiwa kungiyar Hamas da ke iko da zirin Gaza hari saboda harin da ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, ya kuma ce kungiyar Hamas za su iya kawo karshen wannan rikici a yau ta hanyar sako mutanen da suka yi garkuwa da su.

Sai dai ya kira tasirin da Gaza ke ciki a matsayin abin takaici.

"Ina ta aiki ba dare ba rana don ganin an tsagaita bude wuta nan take na tsawon makonni shida," in ji shi.

Yarjejeniyar za ta "dawo da wandanda aka yi garkuwa da su gida tare da sassauta rikicin jinkai."

A halin da ake ciki kuma, Trump ya aika da sakonin da yawa ga Biden a dandalin Sada zumuntansa. Trump ya rubuta cewa "Yana magana da fushi a fuskarsa, wannan hali irin na mutanen da suka san 'ba za su yi nasara ba," in ji Trump. "Haushi da kuwa ba su taimaka wajen farfado da kasarmu ba!"

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG