Shugaban Hukumar Alhazan Alhaji Muhammad Musa Bello, wanda ya sanar da ranar fara jigilar, ya ce hakkin kowani kamfanin jiragen sama ne ya tabbatar cewa kowace fasinja maniyyaciya na da muharrami.
Da ya ke nasa bayanin, jami'in yada labaran MaxAir, wato kamfani mai kaso mafi tsoka na fasinja maniyyatan, Ibahim Dahiru ya ce tuni su ka dau ma'aikatan tantancewa da tabbatar da cewa an bi ka'ida. To amma ya ce su ma hukumomin alhazai nauyin hakan ya rataya a wuyansu.