Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makafin Jihar Naija Sun Koka


Wani makaho da sandarsa.
Wani makaho da sandarsa.

Makafin jihar Naija sun koka da kama su da hukumomi ke yi don hana su bara ba tare da basu wani abu madadin barar ba.

Ana takun saka tsakanin jami'an tsaro da makafi a jihar Naija saboda kakkama su da hukumomi su ka ba da umurnin yi don a hana su barace-barace, abin da makafin ke zargin cewa ana yi ne ba tare da ba su wani abu madadin barar ba.

Wakilinmu a Minna Mustapha Nasiru Batsari ya ruwaito wasu daga cikin makafin na kokawa kan abin da su ka kira rashin adalcin da ake masu ta wajen wannan kamen. Sarkin Samarin Makafi Malam Suleiman Muhammad ya ce akan kama makaho a aje ba tare da ba shi abinci cikin lokaci ba. Haka zalika, Malam Lawal Ahmed dan asalin jihar Katsina da ke bara a Minna ya ce an yi ta yayata cewa an ba su Naira dubu dari biyar-biyar bayan kuwa ko Naira biyar ba su gani ba. Shi Sarkin Makafin Jihar Naija, Alhaji Muhammadu Rabiu Abdullahi ya ce ana ta kama makafi a ko ina a birnin Minna kamar su ba mutane ba, kuma ana karyar cewa ana ba su tallafi.

Wakilinmu ya ce ya yi ta kokarin jin ta bakin jami'an gwamnati, ciki har da Kwamishiniyar Harkokin Mata da Nakasassun ta jihar Naija Hajiya Hasana Adamu, amma ba a dace ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:03 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG