Yayin da yake jawabi ga wannan sabuwar rundunar yaki da masu tada kayar baya babban hafsan hafsoshin sojin mayakan sama Air Vice Marshall Alex Badeh ya gargadesu da su kara daura damarar yaki da wadanda ya kira 'yan ta'ada. Ya ce wadanda ke kai mana hari ba dukansu bane 'yan Najeriya. Akwai mutanen kasashen waje cikinsu. Akwai masu taimaka masu da kudi da kayan yaki daga kasashen waje. Akwai masu turo masu da makamai daga waje.
Yanzu haka hukumomi a jihar Adamawa na cigaba da fadakar da jama'a game da aikin sabuwar rundunar wadda ke da hekwata aYola, musamman mutanen dake kan iyakar Najeriya da wasu kasashe. Kwamishanan Iyaka Alhaji Hamza Bello ya kirawo mutanen dake iyaka da su hada kai da jami'an tsaro da aka turo zuwa jihar ta Adamawa domin a cimma nasara kamar yadda gwamnan jihar ya riga ya bayyana. Can baya gwamnan ya fada cewa mutanen Adamawa masu son zaman lafiya ne masu kuma son cigaban kasar.
Ga karin bayani daga Ibrahim Abdulaziz.