Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiya Lahadi Wani Da Kunar Bakin Wake Ya Halaka Mutane 13 a Maiduguri, Jihar Borno


 Harin kunar bakin wake a Maiduguri
Harin kunar bakin wake a Maiduguri

Jiya Lahadi aka kai hare-hare a cikin birnin Maiduguri a jihar Borno da suka yi sanadiyar mutuwar mutane 13 kana sama da mutane 17 ne suka jikata

: Jiya Lahadi wani dan kunar bakin wake ya hallaka mutane 13 a birnin Maiduguri na arewa maso gabashin Najeriya mai fama da tashe-tashen hankula

Harin, wanda aka kai da yammacin jiya Lahadi, ya kuma raunata wasu mutane 5. Wasu hare-hare biyu kuma da su ka biyo baya, sun raunata mutane sama da 12.

Kungiyar Boko Haram ta hallaka mutane sama da 20,000 a tsawon shekaru 8 da ta yi ta na tayar da kayar baya ga gwamtain Najeriya, a yinkurinta na kafa tsattsaurar daular Islama a yankin arewa mai rinjayen Musulmi. Maiduguri, babban birnin jahar Borno, shi ne akidar ta Boko haram.

Kungiyar rajin kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce tashe-tashen hankulan Boko Haram sun jefa miliyoyin farar hula a yankin na Tabkin Cadi cikin yanayi na matukar bukata. Mutane kimanin milyan 2.3 ne aka raba su da muhallansu a Najeriya, da Kamaru da Cadi da kuma Janhuriyar Nijar, kuma wasu mutanen sama da miliyan 7 na fuskantar karancin abinci.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG