Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yin Aiki Babu Kananan Likitoci Yana da Matukar Wahala


Likitoci da Ma'aikatan Asibiti
Likitoci da Ma'aikatan Asibiti

Yajin aikin da rukunin likitoci masu neman kwarewa a fannoni daban-daban wadanda ke aiki a asibitocin gwamnatin tarayyar Najeriya na ci gaba da gurgunta harkokin kiwon lafiya a kasar, a ddai-ddai lokacin da manyan likitoci da basa cikin yajin aikin ke kokawa kan mummunan tasirin matakan da kananan likitocin suka dauka.

Yanzu haka dai likitocin sun kwashe watani biyu kennan suna wannan yaji na aiki bisa neman a biya masu wasu bukatun su.

Matakin dai ya gurgunta aiyukan kiwon lafiya a Najeriya, masamman ma a Asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya mallakar Gwamnatin tarayya.

A jihar Kano kusan al’amurana sun tsaya a Asibitin Malam Aminu Kano da kuma Asibitin Kashi na Dala.

Daraktan hulda da jama’a, a Asibitin Aminu Kano, Alhaji Aminu Inuwa, yace tunda wani bangare na Asibiti na yajin aiki tabbaci hakika baza’a samu yadda ake so ba kamar yanzu ba’a kwantar da marasa lafiya sai kwai mara lafiya yazo manya likitoci su ganshi ya koma gida.

Daya daga cikin manyan Likitoci Dr. Andrew Oloko, yace “yanayin aiki likita yafi dadi ace kowa da kowa na bakin aiki babu wanda aka rasa, yin aiki babu kananan Likitoci, yana da matukar wahala da gaske."

XS
SM
MD
LG