Masu shirya zaben raba gardama game da batun ‘yancin kan Kudancin Sudan sun ce yawan masu kada kuri’a zai kai 60% wanda zai bada hurumin halatta dukkannin kuri’un da aka kada a zaben raba gardaman da aka gudanar game da makomar yankin.
Wani jami’in hukumar zaben, Su’ad Ibrahim Eissa, ya fadi a wani jawabi yau Laraba cewa yawan wadanda su ka fito zai ma zarce a kalla 60% din da ake bukata.
Saidai an san cewa mutane kusan miliyan 4 aka yi wa rajistar jefa kuri’unsu a wannan zaben raba gardaman da ake da karfin gwiwar zaton cewa zai kai ga yankin na Kudanci Sudan ya balle daga Sudan, ya zama Kasa mai cin gashin kanta
Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana sa ran samin sakamakon wacin gadi zuwa ran 2 ga watan gobe, inda kuma takamaiman sakamako zai samu cikin sati biyu na biye.
Akasarin zaben dai an yi shi ne cikin kwanciyar hankali, kodayake an yi ta samin muggan fadace-fadace tsakanin kabilun da ke daura da kan iyakokin Arewa da Kudu a Gundumar Abyei da ake rikici a akai.