Masu sa ido na kasa da kasa sun amince da ingancin zaben raba gardama kan batun ‘yancin Kudancin Sudan.Tarayyar Turai ta fadi yau Litini cewa wannan zabe na tsawon mako guda na yanke shawara kan makomar kasar ya inganta kuma an yi shi cikin kwanciyar hankali da lumana. Wata tawagar ‘yan sa ido da tsohon Shugaban Amurka Jimmy Carter ke jagoranta ma ta ce yadda aka gudanar da zaben ya dace da ka’idar kasa da kasa. Cibiyar ta Carter ta ce bisa ga sakamakon wuccin gadi ‘kusan babu shakka’ bangaren Kudu da galibinsa Kirista ne da ‘yan gargajiya zai balle daga Arewa da akasarinsa Musulmi ne. Ba a sa ran samun cikakken sakamako sai farkon wata mai zuwa. Idan ‘yan Kudancin suka zabi ‘yancin kai, Kudancin na Sudan zai zame kasa mai cin gashin kai a watan Yuli.
Masu sa ido na kasa da kasa sun amince da ingancin zaben raba gardama kan batun ‘yancin Kudancin Sudan
Masu sa ido na kasa da kasa sun amince da ingancin zaben raba gardama kan batun ‘yancin Kudancin Sudan.